Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ziri - Amurka


Gabatarwa

Zarara ko Ziri Land bridge, zarara/ziri kenan da ta/ya ratsa tsakiyar manyan tekuna tare kuma da sada tsakanin manya-manyan nahiyoyi biyu. Sai dai, idan girmansa ya yawaita tare kuma da samuwar surƙuƙin daji a ciki, to fassarar za ta iya canjawa zuwa laba/labi kamar yadda muka kira zirin Berin (Bering Land Bridge) da laba kasantuwar tsirran da suka lulluɓe shi.

Ma’anar Zarara (Land Bridge)

Oxford Dictionary (2021), sun fassara kalmar Land Bridge da: “Mahaɗar tsakanin tafka-tafkan ƙasashe guda biyu, musamman ma ta zamanin jahiliyya wadda ke bai wa mutane da dabbo damar mulkar sababbin dauloli kafin teku ta raba tsakani, kamar yadda ta faru tsakanin Zararar Berin (Bering Strait) da kuma Mahaɗar Turai”.


Labar Berin
Hoto: National Preserve


Labar Berin
Hoto: National Preserve

Su kuwa Britannica Encyclopaedia (2018), a tasu ma’anar cewa suka yi: “Kowace ɗaya daga cikin zarori (isthmuses) wadda ta sada tsakanin manyan nahiyoyin duniya a mabambantan lokuta, wadda sakamakon haka mabambantan nau’ukan halittun dabbobi da tsirrai suka samu damar faɗaɗa iyakokinsu zuwa wasu sababbin yankuna.” Sai kuma Merriam-Webster (Babu Shekara) da suka bata ma’ana ta: “Zararar ƙasa da ke sadar da tsakanin manya-manyan ƙasashe guda biyu (kamar nahiyoyi ko nahiya da kuma tsibiri)”.


Zirin Panama
Hoto:Live Science

Misali

Kyakkyawan misalin wannan zararara wadda ta samu sakamakon dusar ƙanƙara; a zamanin ƙanƙara, ta zama laba daga baya, ita ce Zarararar Berin wadda ta sada tsakanin Nahiyar Asiya (Asian Continent) da Nahiyar Amurka ta Arewa (North American Continent).

Manazarta:

Britannica, T. Editors of Encyclopaedia (2018, April 17). Land Bridge. Encyclopedia Britannica. An ciro a 2021, daga https://www.britannica.com/science/land-bridge

Graham A. (2018). Land Bridges Ancient Environments, Plant Migrations, and New World Connections. University of Chicago, U.S.A. An ciro a 2021, daga https://press.uchicago.edu/ucp/books/chicago/L/bo27847605.html

Merriam-Webster. (n.d.). Land bridge. In Merriam-Webster.com dictionary. An ciro a 2021, daga https://www.merriam-webster.com/dictionary/land%20bridge

National Geographic (2021). Bering Land Bridge. An ciro a 2021, daga https://www.nationalgeographic.org/photo/bering-land-bridge/

Richardson J. (2018). Climate Shift May Have Spurred Migration Across Bering Land Bridge. University of Alaska Fairbanks.



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub